Yadda Ake Tuwon Biskin Alkhama

Tuwon Biskin alkama yana daya daga Cikin nau’in tuwo na gargajiya daakafi Samunsa a gidan sarakai akasar Hausa kuma yana daya daga Cikin abinci Mai kyau da Gina jiki.

Abubuwan Bukata Wajan Tuwon Biskin Alkhama

  • Alkama
  • Man fari
  • Ruwa

Yadda Ake Hadashi

  • Dafarko a Samu alkama a surfa a busheta Bayan an busheta sai a shanyata arana ya Kara bushewa Bayan ya bushe sai a zurta ta a turmi a bushe ta Bayan a busheta sai a kaita gidan nika anika amma nikan Biski.
  • Bayan Annika sai a sa garin a gitere/madambaci Bayan nan sai a sa ruwa a tukunya a zuba Mai acikin Ruwan sai a Nana giteren/madambaci akan tukunya sai a dora a wuta
  • Bayan ya bugo/ yafara kamshi zai a tukashi a gyarashi da Mara /abun gyaran tuwo sai a sa masa karamar wuta a barshi ya Nuna Har tsawon mintuna talatin sannan a tone shi /kwasheshi a zuba a flasks ko a kwarya Mai tsafta.
Previous article
Next article

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles