https://www.fapjunk.com https://pornohit.net london escort london escorts buy instagram followers buy tiktok followers

Yadda Ake Peanut

Abubuwan Bukata

  • Gyada
  • Flour
  • Sugar 1/2 tbsp
  • Gishiri
  • Vanilla
  • Kwai
  • Madara (milk powder)
  • Mai

Yadda Ake Hadawa

Dafarko za’ayi Sami gyada mai kyau (marar baya/ kwanso a jikinka ) irin wadda Ake suyar gyada da ita sai a gyara ta a fitar da marar kyaun cikinta

Sannan a zuwa gyadar cikin kwano babba sai a zuba gishiri akai sannan a zuba zuwan zafi a juya shi sosai sai a barshi yayi minti biyar

Bayan minti biyar sai a tace gyadar a zuba a cikin flat sai a sata cikin rana har sai ta bushe babu wannan ruwan a jikin gyadar

Sai a dauko Wani kwanon daban a zuba flour, gishiri da Madara ta gari a gaurayashi sai a ajiye a gefe

Sannan dauki Wani kwanon daban a fasakwai a ciki sai a zuba sugar da vanilla a ciki a gauraya har sai sugar da aka zuba ya narke

Bayan nan sai a dauko kwanon da aka zuba gyadar a ciki da kwano da aka hade ruwan kwai sai Kuma kwanon da a hada flour sai asa cokali a ciki(spoon) a dibi zuba kwai a cokali a zuba akan gyada sai ana gaurayawa Amma ba’a sa hannu a ciki za’ana juya(sharking)kwanon ne har ya hade

Sannan a zuba flour acikin ita a gauraya a haka za’ana zuba ruwan kwai da flour a ciki kadan-kadan sai sai gyadar ta kama jikinta

Sai asa mai cikin kasko (frying pan) sai ya Dan yi zafi da Sannan a fara zuba peanut a ciki idan ya soyu sai a tsame

Shikinan an hada peanut

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles