Yadda Ake Hada/Gasa tsire

INGREDIENTS

 • Nama
 • borkono
 • kuli-kuli
 • citta
 • kimba
 • kanunfari
 • masoro
 • thyme
 • curry
 • busashen tafarnuwa
 • da sauran spices
 • Mangyada
 • gishiri
 • maggi sai tsinkan tsire

PROCEDURE

Ki daka dukkanin spices naki tare da kuli, amma kulin ya ďan fi yawa, kuma ki sanya maggi da gishiri. A zabi nama mai kyau wanda babu kitse sosai a jiki, sai ki yanka shi sirara ta kwance da dan tsayi kadan sai ki ďauko tsinken tseren ki jera wannan naman a jiki. Wato in kin huda ta ciki sai ki fitar da shi ta waje. Daga nan sai ki sami kwano ki zuba mangyada dai-dai misali tare da gishiri da maggi kaďan ki shafe jikin naman duka. Kina yi kina sanya shi cikin haďin kulin ya kama jikinsa da kyau. Daga nan in a oven ne sai ki yi ta jera su suna gasuwa. In ma a rushi ne duka ba damuwa.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles