https://www.fapjunk.com https://pornohit.net london escort london escorts buy instagram followers buy tiktok followers

Yadda Ake Hada Awara A Kasar Hausa

Abubuwan Bukata

  • Waken soya
  • Mai
  • Kwai
  • Maggi
  • Gishiri
  • Ruwan tsami/Khal/Tsamiya

Yadda Ake Hada Awara
Dafarko zaa gyara waken soya a zubashi a roba a wankeshi a jikashi a ruwa.

Bayan ya jiku sai a nikashi a blender ko kuma a Kai shi gidan nika . Bayan an nika sai a Kara mishi ruwa a juyashi sai a nemi abun Tatar koko sai a tace nikakken garin waken Bayan antace shi an fidda dusar sai a juyeshi a tukunya babba a dorashi a wuta a rufe.
Sai a zauna a kusa a jira ya tafasa dazarar yafara abun kafasa sai a bude murfin tukunyar sai a Fara zuba ruwan tsami ko kuma ruwan jikakken tsamiya ko a hada farin Khal a ruwa sai a zuba aciki da Zarar an Fara zubawa to a waran zaifara Kama jikinsa sai Ana zuba ruwan a hankali harsai duka Yakama jikinsa.

Dazarar yagama kamawa sai a sake dauko abun Tatar koko da kuma matsami sai a kwashe awaran daga tukunya Ana zubawa a wannan Matacin.
Bayan angama kwashewa sai daure awaran dake Cikin Matacin sai a Dora mishi abu Mai nauyi saboda yayi saurin tsanewa.

Bayan ya tsane sai a cireshi a yayyanka shi.
Daga karshe sai A jika ruwan gishiri da Maggi sa zuba yankakken awaran aciki abarshi na tsawon minti biyar. Sai a cireshi a soyashi a Cikin Mai ko kuma a soyashi da Kwai .

Anacin wara da yaji ko kuma da miyar taruhu da albasa

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles