Yadda Ake Hada Alalar Wake

Alalar Wake (moi moi)

 • Alalar wake dai nau’in abinci ne da keyinsa Duk Africa.Kuma yana daya daga Cikin nau in abinci masu matukar mahimmanci a jikin mutum.

Abubuwan Bukata

 • Wake
 • Tattasai
 • Attaruhu
 • Albasa
 • Maggi
 • Gishiri
 • Man fari ko naja
 • Ruwa

Yadda Ake Hada Alalar Wake.

 • Dafarko zaa jika waken Alala acikin roba Mai tsafta abarshi na tsawon mintuna goma.
 • Bayan ya jiku sai atace a zubashi aturmi a surfashi.Bayan ya surfu sai a sake juyeshi Cikin roba a zuba masa ruwa a wanke Shi ya wanku Har sai anfidda dukkanin dusar daga waken.
 • Bayan anwankeshi yafita Sosai sai a gyara taruhu da tattasai a kuma yanka albasa sai a sa ruwa daidai azanci sai a Kai shi gidan nika.
 • Bayan annikashi sai a zuba Maggi da gishiri da kuma yankakken albasa da kuma Mai da ruwa kadan acikin kullin alalar sai a gaurayashi Sosai.
 • Daga karshe kuma sai a shafa Mai aijikin Leda sannan a zuba kullin alalar a daddaura.
 • Bayan angama daurawa sai a sa a rukunya a zuba ruwa sai a rufe abarshi har sai ya dahu.
 • Za’a iya cin alalar wake da Mai da yaji Koda miyar jajjage.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles