Miyar Taushe

Miyar taushe miyace ta gargajiya da kuma zamani wadda akafi yinta a Nigeria dawasu kasashe na Africa. Miyane ne daya ke Kara lafiya ga jikin mu.

Abubuwan Bukata Wajan Hada Miyar Taushe

 • Ganyen Yakuwa
 • Kabewa
 • Albasa
 • Gyadar Miya
 • Daddawa
 • Nama
 • Maggi Da Gishiri
 • Tafashashen Kayan Miya
 • Garin flour/garin laushi na gero ko masara.

Yadda Akeyi Miyar Taushe

 • Dafarko zaa Samu yakuwa a gyarata a kuma yanka ta Bayan an yanka yakuwa sai a fere kabewa ayanka ta.
 • Bayan an yanka yakuwa da kabewa da albasa sai a wankesu sosai sai asa gishiri kadan Akara wanke ya Kuwar Sosai bayannan sai a zuba wankanken yakuwar da kabewa da kuma albasa da nama da Kayan kamshi a tukunya a Dora a wuta
 • Bayan an Dora sai a zuba tafashashshen Kayan miya da Mai a Cikin tukunya a rufe abarshi ya dahu na tsawon mintuna .
 • Bayannan sai a zuba yar dakkiyar daddawa da dakakkiyar gyadar miya da Maggi da gishiri sai a Kara barinsu ya dahu .
 • Daga karshe kuma sai a hada flour ko dan garin laushi na gero ko masa dankadan a kwano da ruwa sai a zuba ma miyar a garwaya sbd ya daure Bayan minti biyu sai a sauke miya ya Nuna.
 • Zaa iya cin miyar da tuwon biskin alkama ko tuwon shinkafa ko biskin Gero.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles