Jigawa: Tallafin Kudi Ga Mata Masu Juna Biyu

A wani mataki na karfafa wa mata masu juna biyu da masu shayarwa zuwa awo a asibiti, gwamnatin jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta fara ba wa matan Naira 4.000 kowane wata do rage wa matan karkara radadin talauci.

Mata masu juna biyu da wadanda suke da goyo a jihar Jigawa sun fara amfana da tallafin Naira dubu hudu zuwa dubu biyar da gwamnatin jihar ta Jigawa da ke arewacin Najeriya ta yi musu alkawari.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne domin inganta lafiyar yara kanana a cewar Shu’aibu Musa Kafin Gana, shugaban Hukumar kula da muradin tabbatar da lafiyar yara kanana: “Tallafin dubu hudu da gwamnatin jiha ta yi alkawari za take ba mata wanda ta dauka a cikin kasafin kudin shekarar 2021, inda ta saka Naira milliyan dari shida a cikin wannan kasafin kudin, yanzu an shiga lungu da sako na jihar Jigawa da kananan hukumomi 27, an kuma dauki mata 20 kowane bangaren da ake jefa kuri’a wato “political ward” kenan. To idan aka lissafa jimilla za ka ga an samu mata fiye da dubu biyar.

Yanzu haka an raba kudin ne a karamar hukumar Birnin Kudu, matan kuma da suka amfana da wannan tallafi sun bayyana irin farin cikinsu da kuma jin dadinsu tare da kokarin da suke wajen amfani da kudin nasu.

Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu┬áMagaji Yusuf Gigo ya bayyana jindadinsa, inda ya ce “wannan tallafin zai rage radadin da mata masu juna biyu ke ji. Wasu za su yi amfani da kudin a matsayin jari na yin sana’a.”

A wani mataki na karfafa wa mata masu juna biyu da masu shayarwa zuwa awo a asibiti, gwamnatin jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta fara ba wa matan Naira 4.000 kowane wata do rage wa matan karkara radadin talauci.

Mata masu juna biyu da wadanda suke da goyo a jihar Jigawa sun fara amfana da tallafin Naira dubu hudu zuwa dubu biyar da gwamnatin jihar ta Jigawa da ke arewacin Najeriya ta yi musu alkawari.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne domin inganta lafiyar yara kanana a cewar Shu’aibu Musa Kafin Gana, shugaban Hukumar kula da muradin tabbatar da lafiyar yara kanana: “Tallafin dubu hudu da gwamnatin jiha ta yi alkawari za take ba mata wanda ta dauka a cikin kasafin kudin shekarar 2021, inda ta saka Naira milliyan dari shida a cikin wannan kasafin kudin, yanzu an shiga lungu da sako na jihar Jigawa da kananan hukumomi 27, an kuma dauki mata 20 kowane bangaren da ake jefa kuri’a wato “political ward” kenan. To idan aka lissafa jimilla za ka ga an samu mata fiye da dubu biyar.

Yanzu haka an raba kudin ne a karamar hukumar Birnin Kudu, matan kuma da suka amfana da wannan tallafi sun bayyana irin farin cikinsu da kuma jin dadinsu tare da kokarin da suke wajen amfani da kudin nasu.

Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu Magaji Yusuf Gigo ya bayyana jindadinsa, inda ya ce “wannan tallafin zai rage radadin da mata masu juna biyu ke ji. Wasu za su yi amfani da kudin a matsayin jari na yin sana’a.”

Fatima Nuraddeen Hayat, kwararriya ce kuma masaniya a kan yaki da cutar tamowa a jihar Jigawa. Ta bayyana irin tasirin da wannan kudi zai yi ga mata musamman ma masu ciki. “Gaskiya zai taimaka wa matan nan kuma zai taimaka wa rayuwarsu sosai domin mafi yawa a cikin su ba su san ma yadda za su yi da rayuwarsu ba. Muna ganin wanna kudin zai taimaka musu wajen inganta lafiyarsu da kuma sayan abubuwan da za su gina jikinsu da na ‘ya’yansu, masu zuwa talla za su mayar da su makaranta.”

Ka’idar wannan tallafi shi ne kafin mace ta samu wannan tallafi za ta kasance tana da juna biyu, ta kasance tana zuwa asibiti, idan kuma za ta haihu ta je asibiti.

Jihar Jigawa dai tana sahun gaba a Tarayyar Najeriya wajen fama da cutar tamowa ta kananan yara.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles