GYARAN JIKINMU TA KO INA YADDA ZAKI DINGA KYALLI, SANTSI, KAMSHI, MAGANIN KURAJE

SABULUN KURAJE
• asef soap
• pharmaderlm soap
• kanwa
• jar dilka
• Zuma
• lemon tsami
Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun kamar uku ko Dama da haka.

SABULUN FIDDA TABO

 • ko Zuma Zaki Iya shafawa idan Zaki kwanta bacci sai da safe ki wanke da ruwan dumi.
 • misscoroline soap
 • shary soap
 • aloevera soap
 • garin alkama
 • zuma
 • kanwa kadan
 • lemon tsami Bari 1/1

Sai ki goga su ki hada ki zuba Zuma a ciki da lemon tsami da kanwarki ki kwaba, ki dinga shafawa fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma zakiyi wanka dashi Zaki dinga wanke fuskarki.

SABULUN GYARA FATA

idan har kina San gyaran fata kina iya wannan hadin domin gyaran jiki, fatar ki zata yi kyau sossai.

 • sabulun sel
 • sabulun salo
 • lalle
 • zuma
 • garin darbejiya
 • sabulun premier,kurkum
 • sabulun zaitun
 • dudu osun.
 • dettol
 • Zaki daka sabulun duka ki zuba a mazu Bi ki zuba lalle da majigi a Kai da zuma da kur-kur ki juya shi sossai garin darbejiya kuma ganyen Zaki samun ki shanya ki daka ki tankade ki hada akan sabulun ki saka ruwa kadan ki juya yadda zai hade jikinsa Zaki ga yadda fatarki zata canja sirrin kyau.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles