Gyaran Jikin Amare A Saukake

Ga Yanda Zakihada

Idan kamar saura wata guda kiyi aure sai ki rage yawan shiga rana dan kuwa da wuya ki dai na shiga rana gaba daya idan kamar saura sati biyu bikin ki to yar uwa ta sai ki samu

  • Kurkur
  • Madara
  • Kwai
  • Dilka
  • Zuma
  • Lemon tsami
  • Majigi
  • Turaren gaf gaf

Yar uwa ki hada kurkur da madara da kwai ki kwaba su waje daya sai ki shafe duk jikin ki dashi sannan ki barshi yayi kamar awa biyu sai ki samu hankici me kyau ki samu ruwan dumi ki goge fuskar ki a hankali sai ki shiga wanka da ruwan dumi ki wawatsa ruwa a jikin ki amma kar kiyi amfani da soso da sabulu in kin fito sai ki samu dilka ki zuba ruwan zafi ya narke sosai sannan ki zuba zuma ki kuma matse lemon tsami a ciki ki shafe duk jikin ki da shi sai ki turara jikin ki da turaren gafgaf zuwa minti talatin sannan kuma ki shiga wanka da sabulu babu soso haka zaki dinga yi kullum har zuwa lokacin bikin ki zaki ga yadda jikin ki zai goge yayi matukar kyau

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles