Farfesun Kifi Tarwada (Cat Fish)

Farfesu dai abune da ke yinsa .

Farfesun kifi (Cat Fish) abinci dake kunshi da sunadarin protein koma da kara lafiya gagarkuwar Jiki.

Abubuwan Bukata Farfesun Kifi Tarwada (Cat Fish)

 • Kifi (Cat Fish)
 • Taruhu
 • Albasa
 • Kayan kamshi
 • Man fari
 • Lemon tsami
 • Curry
 • Maggi
 • Gishiri

Yadda Ake Hadawa Farfesun Kifi Tarwada (Cat Fish)

 • Dafarko Idan akasamu Kifin an Fiso a wankeshi da lemon tsami saboda fidda Karnin kifin.Bayan an wanke Kifin sosai ya wanku sai a sa man fari kadan a Cikin tukunya sai a sawa man Kayan kamshi da albasa sai a dan soya kamar na second hudu sai a dakko Kifin a sanya shi a cikin tukunyar sai Adan soya kadan na tsawon second hudu.
 • Bayan an dan soya kifin sai a Debo ruwa daidai yadda zai isa sai a zuba a tukunyar Bayan an zuba sai a Kara Kayan kamshi da albasa da curry da Maggi da gishiri da kuma nikakken taruhu da tassai daidai yadda zai isa . Amma wasu basa sa tattasai an fisa taruhun shi kadai ya isa.
 • Daganan kuma sai asanya dakakken daddawa kadan sai a rufe tukunyar.
 • Bayan wasu mintuna sai a duba in ya dahu sai a sauke sbd kifi baida wahalar dahuwa.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles