Bayani Akan Tallafin Karatu na BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA)

Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa wato Federal Ministry of Education a ƙarƙashin tsarin nan mai suna BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) ta buɗe shafin ta domin ɗaukar ɗaliban da za a tura ƙasashen wajen domin yin Degree na farko da na biyu (Master’s Degree) da kuma na uku (PhD) na shekarar 2023/2024.

Ƙasashen da za a tura wanda zasuyi degree na farko, wato undergraduate studies sune: Russia, Morocco, Hungary, Egypt da kuma Venezuela.

Ga kuma courses ɗin da zasu iya cikewa:

  • Engineering, Geology, Agriculture, Sciences, Mathematics, Environmental Sciences, Sports, Law, Social Sciences, Biotechnology, Architecture, Medicine (very limited), Pilot Engineering, and Neurologist.
  • Ƙasashen da za a tura masu degree na biyu dana uku wato Postgraduate studies sune: Russia (ga waɗanda sukayi degreen su na farko a Russia), China, Hungary, Serbia, da kuma Romania.
  • Masu Master’s degree da PhD zasu iya cike kowanne course.
  • Wanda zaiyi applying na undergraduate dole ne ya zamanto yana da distinction guda bakwai (As&Bs) a WAEC ɗinsa ta shekarar 2021/2022 sannan kada ya gaza shekara 17, kada kuma ya wuce shekara 20.
  • Post graduates kuma dole ya zamanto kana da First Class ko kuma 2nd Class Upper a degree na farko.
  • Dole ka mallaki NYSC discharged certificate and the age limit is 35 years for Masters and 40 years for PhD.
  • Zasu rufe ranar Juma’a 6th January, 2023.

Links ɗin da za a shiga domin applying shine

https://fsbn.com.ng/scholarships

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest Articles